ArewaHitsMusic: SLM malam ajasu
Ajasu: Wslm ranka ya dade
ArewaHitsMusic: Kawuni lafiya?
Ajasu: Lfy lau ranka yadade amma ina cikin far gaba
ArewaHitsMusic: Wani irin far gaba kenan?
Ajasu: Eh to kila kunji lbr abakin Al,umma koh a gari cewa an kawo min mummunan Hari da dare misalin karfe 9
ArewaHitsMusic: Toh! A ina kenan?
Ajasu: Anyi invite nawa show soba bayan nagama performance na wakokina tare da yarana a soba sai mu biyo hanya akan mudan motsa kafa ni da yarana saboda na kwana biyu banyi tafiya mai nisa a Kafa ba
ArewaHitsMusic: Harinda'aka kawoma na makamai ne kokuma anso aimaka dukan tsiya ne?
AjasuKwatsam bazato ba tsammani sai muringa. Jin zagi tabayan mu ana zagin sunan mahaifiyata sai nace ma yarana Kada su kula su saboda bana kaunar tashin Hankali a rayuwa na don Harinda suka kawo min da makamai a hannun su sannan a cikin su sun rufe fuskan su Wanda idon su Kawai ake iya gani
ArewaHitsMusic: Allah sarki ko akwai wa'inda bakwa shiri ne a soban?
Ajasu: Kowa nawa ne a soba, suna sona kamar yadda suke son Kansu domin a rayuwa na ban taba yin fada ba balle ace Ajasu yana da Abokin fada
ArewaHitsMusic: Taya kuka samu kuka tsira toh
Ajasu: Allah ne ya kawo jama,a sai suka kyale mu, acikin su mun gane mutane uku Sai naje nayi report a police station, sannan naje gidan iyayen yaran nagaya musu
ArewaHitsMusic: Koma baka tunanin ba chune akaima ba?
Ajasu: E nayi tunanin haka
ArewaHitsMusic: Yanzu idanda wani abu yasame ka kana tunanin zaka daina waka
Ajasu: Gaskiya bana tunanin zan daina waka saboda jin cewa ankai mun Hari hankalin masoyana ya tashi har wasu suna debo makamai dakyar na samu na shawo Kansu tare da Yan sanda da sojoji da suka zo garin akan maganan
ArewaHitsMusic: Gaskiya kanada masoya ajasu
Ajasu: Mun gode Allah so sai wasu daga Wani state din sun zo min Allah ya kyauta kamar jigawa da kano,bauchi katsina,Jos Kaduna duk sun zo soba, hakan yasa yanzu Zan kara dagewa akan wakana dan faranta ran masoyana
Monday, 16 October 2017
An Interview


0 Response to "INTERVIEW: AJASU WAS ATTACKED IN SOBA"
Post a Comment